Sanatan ya fadi haka bayan ya kai ziyarar jaje a garin Dalori daya daga cikin mazabarsa inda mayakan Boko Haram suka kashe mutane sama da 80 tare da kona gidaje.
Yayin da Gwamnatin kasar ke kokarin gani ta kawar da kungiyar Boko Haram,inda rundunar Sojin Najeriya tace ta kaddamar da bincike kan hare haren da mayakan Boko Haram suka kai da yayi sanadin mutuwar rayukan jama’a da dama a kauyukan da ke kusa da garin Maiduguri a ‘yan kwanakin nan.
Rundunar sojin ta fadi a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa ta fara bincike akan hare haren amma ba tare bayar da cikakken bayani ba.288